Masarautar Katsina ta nada tsohon ministan sufurin jiragen sama, Sen. Hadi Sirika, da dan Gwamnan jihar Dikko Radda mai suna Umar, da wasu mutane hudu a matsayin Hakimai.
Nadin nasu na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren masarautar Alhaji Bello Ifo ya fitar a Katsina.
A cewar sanarwar, Sirika shine sabon Hakimin Shargalle a karamar hukumar Dutsi, yayin da Umar ya kasance Sabon Gwagwaren Katsina kuma Hakimin Radda ta karamar hukumar Chirnacin jihar.
Haka zalika an nada Alhaji Ahmad Abdulmumin Kabir Sabon Dan majen Katsina kuma hakimin Dankama dake karamar hukumar Kaita.
Sanarwar ta kara cewar nadin nasu ya fara aiki ne tun daga jiya asabar.
