Sarkin ya kuma yi kira ga jama’ar Kano su zauna lafiya duk da kokarin da ake na tayar fitina sakamakon hukuncin
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II yayi bayyana hakana ne a wannan jawabi da yayi a yammacin Juma’a, bayan da Kotun Daukaka kara dake Abuja ta yanke hukunci kan danbarwar sarauta jihar.
“Kamar yadda aka sani, masarauta ta samu nasara a Kotu, a inda Kotun Daukaka Kara, ta tabbatar da cewa, Kotun Tarayya ba ta hurumi da za ta sa baki a kan masarauta.
“Wannan hukunci, hukunci ne wanda dama sananne ne. (Domin) su wadanda suke je kotun, sun san cewa kotun ba ta da hurumi. Shi alkalin da ya ba da oda, ya san ba shi da hurumi. Wadanda suka sa alkalin ya bada odar su san ba shi da hurumi.
“Amma yau wata takwas aka ka bayar da odar domin a kawo son zuciya, a kawo fitina a wannan kasa”. Inji Sarkin
Sarkin ya dangana babar nasarar da suka samu ita ce, Allah Ya kare rayukan mutanen jihar Kano, kuma Allah Ya tsare su daga tashin hankali.
Sannan yayi kira ga mutanen Kano da a ci gaba da kiyaye wannan zaman lafiyan da aka san jam’ar jihar da ita.
Domin a cewarsa, wannan yaki ko rigima ba da su ake yi ba, da hukuncin Allah ake yi.
Sarkin ya kammala jawabinsa da addu’ar duk mai neman tashin hankali a jihar Allah Ya mayar kansa.
“Kuma duk wanda ke neman ya hura wuta a Kano, Allah Ya sa wutar ta kone shi. Duk wanda yake son ya tayar da hankalin mutanen Kano, shi ma Allah Ya tayar masa da hankalinsa”. Inji shi
Tun bayyana hukuncin kotun ne a ranar Juma’a mutane suke ta bayyana farin cikinsu tare da yin dafifi a Kofar Kudu, a cewar rahotanni.