Daga Ahmad Hamisu Gwale
Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi na II ya fito domin fara jagorantar zaman fada na Juma’a a fadar Sarkin na Kofar Kudu.
Wannan na zuwa ne bayan da jami’an tsaro suka mamaye gidan Sarkin tare da hana shi fita don tafiya masarautar Bichi kamar yadda aka shirya .
Kawo yanzu haka Sarkin ya zauna domin fara jagorantar zaman fadar domin karbar gaisuwa daga hakimai da sauran baki kamar yadda ya saba.
An rawaito cewa jami’an tsaron sun hana shige da fice zuwa fadar ciki har da wasu jami’an gwamnati da hakimai
Sarkin ya fito cikin ado a kan doki daga cikin gida zuwa inda yake zaman fada, inji wakilinmu.
Babu tabbacin su wadanda suka bayar da umarnin girke jami’an tsaron a fadar Sarki tare da hana shi fita, sai dai ana zargin ‘yan hamayya da gwamnatin Kano da kuma masarauta da hannun a wannan batun.
Gwamman Kano Abba Kabir Yusuf ba ya gari tun tafiyar da yayi ziyarar aiki a kasar Indiya