
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi tare da wasu manyan hakimansa a yayin rangadi
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya sake fita rangadi zuwa gundumoni na wasu kananan hukumomin jihar Kano
A zagaye na biyu na rangadin sarkin zai je Dawakin Tofa da Tofa ranar Asabar sai kuma Kabo da Rimin Gado a ranar Lahadi.
Tuni sarkin ya isa Dawakin Tofa a ranar Juma’a inda ya jagoranci sallar juma’a a babban masallacin juma’ar garin gabannin babban taron ganawa da jama’ar kasar Dawakin Tofa a kofar gidan hakimi a washegarin Asabar.
A makon da ya wuce ne sarkin ya kai irin wannan ziyarar Karamar Hukumar Danbatta da Makoda da Ungoggo da kuma Minjibir a inda ya gana da al’ummar kasahen hudu tare na gundumomin Kunya da kuma Zaura Babba