
Sarkin Kano na 16 muhammadu Sanusi na biyu ya yaba da irin rawar da hukumar Hisba ke takawa wajen kyautata tarbiyya da kuma kare martabar al’umma.
Sarkin ya kuma bukaci hukumar da ta samar da kundi na musamman da za a rika adana bayanan batun sakin aure, domin rage matsalolin da ke addabar aure a tsakanin jama’a.
Sarkin ya shawarci hukumar Hisba da ta kirkiri asusu na bayar da rance ga mazajen da suka rabu da matayensu don bayar da kudin ciyarwa ga yara, inda iyayen za su dinga biya a hankali.
Ya yin ziyarar kwamandan Hisba Mal Aminu Ibrahiim Daurawa wanda mataimakinsa Dr. Mujahid Aminuddini ya yi, ya ce sun kawo ziyarar don neman shawarwari kan cigaban al’umma.
Mujhid ya kuma bayyana ce wa tini Gwamnatin Kano tayi musu alkawarin karin albashi da samar da kayan aiki ga hukumar.