
Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate, ya bayyana cewa fiye da likitoci 16,000 ne suka bar Najeriya cikin shekaru biyar zuwa bakwai da suka gabata, domin neman ingantaccen yanayin aiki a ƙasashen waje.
Ministan ya fadi hakan ne a jawabinsa a taron horas da Ƙungiyar Likitocin Afirka a Abuja, a farkon makon nan.
Ministan ya bayyana damuwarsa game da yadda hakan ke shafar tsarin kiwon lafiya a ƙasar.
“Nas-nas da unguwarzoma na cikin waɗanda suka bar ƙasar lamarin da ya ƙara rage yawan ma’aikatan lafiya da ake da su a cikin gida.
“Kididdiga ta nuna cewa ikita huɗu ne ke duba mutane dubu 10 a Najeriya, kuma ana kashe sama da dala 21,000 wajen horas da kowanne likita guda”. In ji Ministan.
Minista Pate ya jaddada cewa yawancin kwararru na ficewa ne saboda matsalolin tattalin arziƙi da rashin kyawun yanayin aiki da buƙatar samun ƙarin horo da kuma samun damar gudanar da bincike a sabbin wuraren ayyukansu a ƙasashen waje.
Ministan ya bayyana cewa, kodayake ficewar likitoci daga ƙasashe masu tasowa zuwa ƙasashen da suka ci gaba ba sabon al’amari ba ne, amma yawan da hakan ke faruwa a Najeriya a ‘yan shekarun nan ya karu fiye da yadda aka saba.