
Sabon Sakataren Gwamnatin yana karbar takardar kama aiki daga gwamnan Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba shi takardar kama aikin ne a ranar Litinin a wani kwarya-kwaryar biki a gidan gwamnati
Sabon Sakataren Gwamnatin Kano Umar Faruk Ibrahim ya kama aiki a ranar Litinin.
Sakataren ya karbi takardar kama aiki a safiyar ranar a ofishin gwamnan jihar a wani dan kwarya-kwaryar biki.
A ranar Asabar dadaddre aka sanar da nadin Sabon Sakataren Gwamnatin a wata sanarwar da Sunusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun gwamnan ya fitar.
Nadin na zuwa ne watanni biy bayan sauke Dakta Abdullahi Bichi daga mukamin a wani garambawul da gwamnan ya yi wa majalisar zartarwar jihar.