
Sabon kwamishinan ‘yan sandan Kano Ibrahim Adamu Bakori ya kai ziyarar gani da ido kasuwar Kwalema dake unguwar Dakata, inda aka samu tashin gobara a safiyar Laraba
Gobarar ta kone shaguna da dama a kasuwar, wanda hakan ya janyo asarar dukiya mai tarin yawa.

Kwamishinan ‘yan sandan ya bada umarnin gudanar da bincike don gano dalilin tashin gobarar.