Sabon Hafsan Sojan Ƙasa Laftanar Janar Waidi Shaibu ya kai ziyarar aiki karon farko birnin Maiduguri domin ganawa da rundunar yaƙi da Boko Haram.
Yayin ziyarar ta kwana biyu, janar ɗin ya yaba wa rundunar Operation Hadin Kai bisa “ƙoƙarinsu na yin amfani da sababbin dabaru wajen yaƙi da ‘yanbindiga”, kamar yadda wata sanarwa daga rundunar ta bayyana.

- Babban hafsan soji ya ƙaddamar da rundunar magance matsalar tsaro a jihohin Filato da Bauchi da Kaduna
- Shugabannin tsaron kasashen Afirka 54 na taro a Abuja kan hanyoyin magance matsalolin tsaro a Nahiyar

Haka zalika, ya yi alƙawarin inganta walwala da kuma kyautata aikin dakaru a fadin Najeriya. Ya kuma kai wa Shehun Borno ziyara Dr. Abubakar Umar Garbai El-Kanemi a fadarsa.
A makon da ya gabata ne Janar Shaibu ya kama aiki a matsayin hafsan sojan ƙasa bayan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya maye gurbin hafsoshin rundunar sojin ƙasar da sababbi.
