Gwamnatin Kano za ta farfado da asusun tallafawa harkokin tsaro na jihar.
Kwamishinan Kula Da Ayyukan Na Musamman, Nasiru Sule Garo ne ya bayyana hakan a zauren majalisar dokokin Kano bayan kare kasafin kundin Hukumar.
Ma’aikatar za kuma ta kirkiro asusun tallafawa matasan jihar da hanyoyin samun aiki, wanda zai taimaka matuka wajen sanin halin da matasan kano suke ciki ta bangaren sana’a da kuma nema musu mafita.
Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin za ta farfado da shirin lafiya jari wanda aka samar a tsohuwar gwamnatin Sanata Rabi’u kwankwaso domin ci gaba da tallafawa al’ummar Kano.
Ana sa rai wadannan shirya-shirye za su taimaka wajen inganta tsaro da samar da ayyukan yi tsakanin matasa.
