
Majalisar dokokin Kano ta fara shirin samar da wata doka wadda za ta bawa sashin gwajin jini da sauran gwaje-gwaje a asibitocin gwamnati da masu zaman kan su ikon cin gashin kan su, domin dacewa daidai da zamani.
Yunkurin hakan ya biyo bayan kudurin da Shugaban kwamitin lafiya na zauren, kuma dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kura da Garun Malam Zakariyya Alhassan ya gabatar.
A cewar Zakariyya idan har majalisar ta samar da dokar kuma gwamna Kano Abba Kabir Yusuf ya Sanya mata hannu ta fara aiki, zata kawo taimako da mafita akan matsalolin da suka yi katutu a bangaren a asibitoci.
Zakariyya yace samar da dokar zai tilastawa ma’aikatan gwaje-gwajen tsayawa a iya bangaren da suke da kwarewa akai, kuma zai kawo karshen umarnin da suke jira daga wasu sassa ko aiki a karkashin wani sashe wanda hakan yake haddasa Rashin fahimta a aikin su.
Wakilin mu Kamal Umar ya rawaito cewar, majalisar ta ce zata gaggauta yiwa kudurin dokar karatu na farko da na biyu cikin gaggawa domin kyautata fannin lafiyar jihar Kano.