
Rundunar ’yan sandan Kano ta kama mutane hudu da ake zargi da hannu a satar Adaidaita Sahu a jihar, ciki har da wata mace, tare da kwato guda shida daga hannunsu.
Wannan na cikin wata sanarwa da muƙaddashin kakakin rundunar, DSP Hussaini Abdullahi, ya fitar a ranar Alhamis.
Bincike ya kai ga kama Suleiman Lawal (Aljan) da Muhammad Tajuddeen da ake zargi da karɓar baburan da ake sacewa, tare da kwato Adaidaita Sahu guda shida.
Sanarwar ta ce an kama Auwal Mohammed mai shekaru 30 da Maryam Ibrahim mai shekaru 25 a karamar hukumar Kura, bayan sun yi yunkurin shake wani direban Adaidaita Sahu, inda suka sheƙa masa guba domin su sace babur ɗin.
DSP Hussaini ya bukaci duk wanda aka sace Adaidata sahunsa ya tuntubi hedikwatar ’yan sanda a Bompai domin tantance kayan da aka kwato.