
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, ta yi watsi da karar da Sanata Rabi’u Kwankwaso ya shigar yana kalubalantar shugabancin jam’iyyar NNPP.
Kwankwaso na karar Cif Dakta Boniface Aniebonam da shugaban jam’iyyar na kasa Dr. Agbo Major kan halascin shugabancinsu.
Dakta Ahmed Ajuji da wasu mutane 20 ne suka shigar da karar ikon kwamitin amintattu na jam’iyyar NNPP (BoT) da shugabancinta, ciki har da Barista Tony Christopher Obioha da Kwamared Oginni Olaposi Sakatarenta na kasa da Cif Felix Chukwurah Mataimakin Shugabanta Kasa.
Masu karar sun bukaci kotun ta hana wadannan jami’an gudanar da taro, ko gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa da kuma da’awar cewa an kore su daga jam’iyyar NNPP.
Mai shari’a M.A. Hassan ya ce, kotun ba ta da hurumin sauraron karar, yana cewa al’amuran shugabanci da zama mambobin jam’iyya al’amura ne na cikin gida.
“Matsayin dokar, kamar yadda kotun daukaka kara da kotun koli suka amince da shi, a bayyane yake, kotuna ba sa yanke hukunci kan al’amuran da suka shafi cikin gida na jam’iyyar siyasa, sai dai a shari’o’in da suka shafi gabatar da ‘yan takara a zabe,” In ji Mai shari’a Hassan.
Lauyan wadanda ake kara, Segun Fiki Esq, ya yi maraba da hukuncin, inda ya bayyana karar a matsayin yunkurin sauya shugabancin jam’iyyar a Shari’ance.
“Kotu ta yi magana a fili-wannan maganar ba ta dace ba, an tabbatar da halastaccen shugabancin jam’iyyar NNPP, kuma a yanzu muna sa ran hukumar INEC ta amince da kuma ba da hadin kai ga jami’an da aka zaba na jam’iyyar,” in ji Lauyan.
Hukuncin ya yi daidai da hukuncin da babbar kotun jihar Abia ta yanke a baya (Kara mai lamba: HUZ/11/2024), ta zartar a ranar 1 ga Nuwamba, 2024, wadda ta mayar da kwamitin amintattu na jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin Dokta Boniface Aniebonam.
Wannan hukuncin ya kuma tabbatar da sahihancin taron jam’iyyar da babban taron kasa.