Kawo yanzu babu tabbas kan ranar da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf zai koma jam’iyyar APC.
A baya dai an ayyana yau Litinin 12 ga Janairu na shekarar 2026, a matsayin ranar da zai bayyana ficewar sa daga jami’iyyar NNPP tare da komawa jami’iyyar APC a mazabarsa ta Ɗiso dake ƙaramar hukumar Gwale a birnin Kano.
A wata hira da wakilinmu Kabir Bello Tukur yayi da shugaban jam’iyyar APC na mazabar Ɗiso, Malam Maje Kabir, yace babu wanda ya tuntubesu kan zuwan gwamnan na Kano zuwa ofishin jam’iyyar ta APC a yau Litinin, domin yin rajista tare da yankar katin shaidar zama sabon dan jam’iyyar APC kamar yadda ake yadawa
Sai dai shugaban jam’iyyar APCn yace a shirye mazabar take ta tarbi gwamna Abba Kabir Yusuf, a duk lokacin da ya yanke shawarar karbar katin jam’iyyar.
A wata ziyarar gani da ido da wakilan Premier Radio suka kai Ofishin jam’iyyar APC na mazabar Ɗiso a jiya Lahadi, sun iske yadda ofishin ya sha sabon koren fenti mai haske da sauran gyare gyaren da suka wajaba
