
Rasha ta kai hari mafi girma a Ukraine tun bayan da aka fara yaƙi tsakanin ƙasashen biyu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane huɗu, ya kuma lalata gine-ginen gwamnati, harin da shugaba Volodymyr Zelensky ya ce zai iya tsawaita yaƙin.
Rasha ta kai harin ne ta sama a inda ake iya hango hayaƙi da ke tasowa daga wani ginin gwamnati da ke ɗauƙe da ofishin ministocin Ukraine a tsakiyar birnin Kyiv.
Karo na farko kenan da aka taɓa wannan ginin tun da aka fara wannan yaƙi shekaru uku da rabi da suka wuce.
Firaministar Ukraine, Yulia Svyrydenko ta wallafa wasu hotunan bidyo da ke nuna yadda aka lalata wani ginin gwamnati, inda ta ke cewa za a iya gyara ginin, amma banda rayukar da maƙiya suka salwanta.
Rundunar sojin saman Ukraine ta ce, daga cikin daren Asabar zuwa safiyar Lahadi, Rasha ta cilla aƙalla jirage marasa matuƙa 810 da makamai masu linzami 13 zuwa cikin Ukraine.
“Harin makami mai linzamin da jirage marasa matuƙa sun haddasa ɓarna a sassan arewaci da kudanci da kuma gabashin ƙasar, ciki har da biranen Zaporizhzhia da Kryvyi Rih da Odesa, da kuma yankunan Sumy da Chernihiv”. In ji Shugaba Volodymyr Zelenskiy
Gwamman dubbai ne aka kashe, kana miliyoyi suka arce daga gidajensu a yaƙi mafi muni da Turai ta taɓa fuskanta tun bayan yaƙin duniya na biyu.