
Sarkin Ingila da Sarauniya Camila a yayin buda baki a wani taro a Ingila (Hoto: The National)
Shekara 1000 ke nan rabon da gidan sarautar Ingila ta yi wa musulmi haka, an kuma yi kiran sallah a cikin fadar da ba taba yi ba a tarihin gidan sarautar

An gudanar da liyafar buda bakin ne a Fadar Windsor Castel a inda kimanin musulmai sama da 300 suka halarta ciki har da wadanda ba musulmai ba.
An zaunar da mahalarta buda bakin ne a katafaren zauren liyafa na Saint George a inda sarakin yake tarbar manyan sarakuna da attajirai na duniya.

BBC shashen Turanci ya rawaito cewa, an yi kiran sallah a cikin fadar a lokacin da rana ta fadi sannan aka yi buda baki da dabinio da kuma ruwn kwakwaka kafin daga baya a rarrab abinci.
Wata kungiyar musulmai ta kasar ce ta shirya liyafar buda bakin tare da amincewar sarkin na Ingila.
