
Wani sabon rahoto da Cibiyar da ke sa ido kan harkokin tsaro a kasar nan ta fitar, ya bayyana cewa a tsakanin watan Yulin shekarar 2024 zuwa watan Yunin shekarar 2025, an yi garkuwa da mutane 4,722 a fadin ƙasar nan.
Rahoton ya nuna cewa an kuma biya kudin fansa da ya kai Naira biliyan 2 da miliyan 570 domin a sako waɗanda aka yi garkuwa da su.
Wadannan alkaluma na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a ke ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro, duk da irin matakan da gwamnati ke ikirarin dauka.
Wani masanin tsaro Manjo Muhammad Bashir Galma (mai ritaya) a zantawar sa da wakilin mu, yace wannan rahoto ya sake fito da yadda tsaro ya kara tabarbarewa a Najeriya.
A nasa tsokacin wani mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum a nan Kano, Dr Nazifi Wada Salisu ya bayyana cewa bayanan da cibiyar ta fitar na da ban tsoro
Wakilin mu Ishaq Sani Dambazau ya ruwaito cewa Ko a makon da ya gabata mai bawa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro Mal Nuhu Ribadu ya gabatar da mutane 128 da aka ceto daga hannun ƴanbindiga a Zamfara.