Hukumar EFCC ta tsare wasu jami’an Hukumar Tattara Kudin Shiga ta Jihar Katsina su biyar, bisa zargin almundahanar fiye da Naira biliyan daya.
Mai Magana da yawun hukumar ta EFCC Dele Oyewale, ne ya tabbatar da kama wadanda ake zargi a Abuja ranar Litinin,
Ya kuma ce, mutanen sun yi sama da fadin jimalar kudi Naira bilyan 1,294,337,676.53k.
Jami’an na EFCC reshen Kano, sun kama mutanen da aka bayyana da Rabi’u Abdullahi, Sunusi Muhd Yaro, da Ibrahim M. Kofar Soro da Ibrahim Aliyu da kuma Nura Lawal Kofar Sauri.
Kuma an kama su ne biyo bayan korafin da gwamnatin Katsina ta shigar.
Ya kara da cewa kudin da aka karkatar an same su ne daga hukumar lafiya ta duniya (WHO) da wata kungiya mai suna Medicins Sans Frontiers and Alliance for International Medical Action (ALIMA).
Mai Magana da yawun EFCC ya ce, binciken da suka gudanar ya nuna yadda mutanen suka hada kai tare da bude asusun banki daban wanda a shine suke karkatar da kudin.
Dele Oyewale ya kuma ce, wanda aka kama suna tsare a ofishin hukumar dake nan Kano kuma da zarar sun kammala bincike zasu gurfanar da su a gaban kotu.