Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya ce, ya daukaka kara kan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke a shari’ar da ake yi kan masarautar Kano.
Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Dan Agundi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Lahadi.
“Babu wani dalili da zai hana mu daukaka kara saboda ba mu gamsu da hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yi a kan batun masarautar Kano ba”. inji shi.
Sarkin Dawaki Babba ya kuma ce, bai ga dalilin da za a hana su daukaka kara kan wannan batu ba.
“Idan har wani gwamna ko minista ko wani dan Najeriya zai yi sata ya kwashe kudin ‘yan kasa, EFCC ta kama shi amma ya garzaya kotu ya nemi a ba shi fundamental Human right …
“Sannan mu da muke rike da sarautar gargajiya, muke kuma rike da abubuwa na addini, abubuwa na doka muna aiki babu ko sisi, sai dan abin da ake bamu, sai a ce ba zu mu daukaka kara ba, akwai adalci a wannan?…
“Tun da sun yi wannan hukunci, to mu bamu hakura ba… Muna da iko da mu yi appeal na cewa ba mu yarda ba. Kotun Allah Ya isa za mu. Idan ta yi hukunci na karshe sai mu hakura mu bar wa Allah. Inji shi.
Aminu Babba ya ce, tuni sun mika tarkardunsu na daukaka kara a Kotun Koli kan wannan batu.
Kuma za su nemi a dakatar da aiwatar da hukuncin da Kotun Daukaka karar ta yi har sai Kotun Kolin ta yanke hukunci ko iya tsawon shekara nawa ne.
A ranar Juma’a ne Kotun Daukaka Kara a Abuja ta sanar da hukuncin da ta yanke a inda a ciki ta ce, Babban Kotun Tarayya da ba ta hurumin a shari’ar baki dayan ta.
Sannan ta umarci da a dawo da shari’a ga Alkalin-Akalai na jihar Kano, shi kuma ya sake ba wani alkalin ya sake sauraronta da kuma yanke hukunci tare da ba Aminu ado damar kare kansa, kamar yadda ya yi korafi.
Wanda hakan masu fashin baki ke cewa, ya tabbatar da nasarar gwamnatin jihar Kano da kuma sarkin Kano Muhammadu Sunusi a dambarwar da aka kwashe sama da watai Takwas ana yi.