Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, sun rabu da matarsa, Cristina Serra, bayan sun shafe shekara 30 suna tare.
Rabuwar da aka yi tsakanin Pep da Cristina an yi ta cikin lumana da fahimtar juna kamar yadda jaridu a Sifaniya suka rawato.
Mutum biyun sun yanke shawarar kawo karshen auren nasu ne tun a watan Disamba, sai dai iya makusantansu ne su ka san labarin rabuwar.
A shekau 2019, Serra ta bar birnin Manchester tare da daya daga cikin ƴaƴansu domin komawa Barcelona don kula da kasuwancin kayan kwalliyarta.
Guardiola da Serra sun hadu a shekarar 1994, lokacin da ya ke da shekara 23 ita kuma ta na da shekara 20, amma sai shekarar 2014 sanann suka yi aure.