Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta kasa ta bayyana cewa matatar Dangote ta samar da lita miliyan 32.02 na man fetur, a cikin Disamba 2025, daga cikin jimillar lita miliyan 63.7 da Nijeriya ta yi amfani da su a lokacin.
Wannan na kunshe ne a cikin wata Takardar bayanai da hukumar ta fitar inda tace matatar Dangote ta kai kashi 71 cikin 100 na aiki a watan, daga burin lita miliyan 50 da ta sanya, yayin ya karu daga lita miliyan 19.5 zuwa kusan lita miliyan 32 a rana.
Hukumar ta ce bayanan ba su hada da ajiyar man fetur da matatar ta ware wa kasuwar cikin gida ba, domin alkaluman amfani sun ta’allaka ne da man da aka kai kasuwa ta hanyar manyan motoci. Ta kuma tabbatar da cewa matatun NNPC uku ba su samar da fetur ba, duk da cewa an fitar da tsohon dizal daga matatar Fatakwal kafin rufewarta a Mayu 2025.
Rahoton ya kara da cewa saboda bukukuwan karshen shekara, an shigo da lita miliyan 42.2 a rana domin cike gibin bukatu, yayin da wasu kananan matatu suka cigaba da samar da dizal.
Hukumar ta ce wadannan bayanai na nuna ci-gaban Nijeriya wajen rage shigo da man fetur daga waje da karfafa samarwa a cikin gida.
