Rundunar ’Yan Sanda a nan Kano ta sanar da dakile yunkurin safarar abubuwan fashewa da miyagun kwayoyi a samame biyu daban-daban bayan samun bayanan sirri, inda aka kama wani mutum tare da kwato abubuwa masu hatsari.
Wannan bayani na kunshe ne cikin sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a jiya Alhamis, 15 ga Janairu 2026, a madadin Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori.
Samame na farko, wanda aka gudanar a ranar 13 ga Janairu, 2026, jami’an ’yan sanda daga Rukunin Rijiyar Lemo sun aiwatar da sammacin bincike a wani gida da ke Tudun Bojuwa, inda aka gano manyan buhuna biyu dauke da abubuwan da ake zargin na laifi ne.
A samame na biyu kuma, jami’an sashen Anti-Daba na rundunar, yayin sintirin leken sirri a Sani Mainagge Quarters da ke Karamar Hukumar Gwale, sun tare wani matukin adaidaita sahu da ke dauke da buhuna uku na abubuwa masu nauyi da ake zargin kayan laifi ne.
Sanarwar ta ce bayan duba na tsanaki kwararrun kan sha’anin bom sun gano abubuwan wasu na’urorin kunna abubuwan fashewa ne har 3,700.” Daga bisani, matukin adaidaita sahun ya jagoranci ’yan sanda zuwa ga cafke wani mutum mai suna Ibrahim Garba, wanda aka fi sani da Manyan Baki, mai shekaru 49, dan Jihar Zamfara.
Ya bukaci al’umma da su ci gaba da kai rahoton duk wani motsi, da ake zargi zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa, tare da gargadin kada a taba duk wani abu da ake zargi, sai a nisanta kai a gaggauta sanar da ’yan sanda.
