‘Yansanda a jihar Kwara sun kama wani mutum mai suna Sylvester Enemo da zargin kashe wata mai ciki Esther Enemo a Ilorin babban birnin jihar.
Rahotonni sun ce matashin mai shekara 29 ya daddatsa gawar matar mai shekara 39 ne, wadda kuma aka ce matar ɗan’uwansa ce, bayan ya halaka ta a unguwar Temidire ranar Laraba.
Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa mijin matar ya yi tafiya a lokacin da lamarin ya faru.
“Ƙarin bincike ya sa an gano sassan jikin matar da aka zuba a wani buhu kuma aka jefar a ƙarƙashin wata gada,” a cewar sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta fitar.
Ta ƙara da cewa jami’anta sun kai gawar Esther asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin.
