Kungiyar Tarayyar Turai (EU) tare da abokan huldarta a Najeriya, ta kaddamar da sabuwar cibiyar kirkire-kirkire da fasahar zamani a Kano, wacce za ta mayar da hankali wajen horas da mata masu kasuwanci.
Cibiyar za ta zama matattarar horo da fasahar zamani ga mata, inda za su sami damar koyon dabaru da fasahohi na zamani don habaka kasuwancinsu.
EU ta bayyana wannan mataki a matsayin wani muhimmin ɓangare na karfafa shigar mata cikin harkokin tattalin arziki.
Shugabar Sashen Tattalin Arziki ta ofishin EU a Najeriya da ECOWAS, Inga Stefanowicz, ta yaba da hadin gwiwar da ya bai wa wannan shiri damar ganin wannan rana.
Ta kara da cewa mayar da hankali kan kirkire-kirkire ya samo asali ne daga tarihin masana’antar yadin Kano.
A nasa bangaren, Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Gwarzo, ya yaba da shirin tare da tabbatar da kudirin gwamnati na bude sababbin hanyoyi ga mata.
Ya ce, “Gwamnati na aiwatar da shirye-shirye na horas da mata a dukkan kananan hukumomi 44 da ke jihar Kano domin inganta dabarunsu.”
