
Gwamnatin tarayya ta ce za ta ɗauko hayar kwararrun jami’an tsaro daga ƙetare don horas da sojojin Najeriya dabarun fada da kwato wadanda aka yi garkuwa da su.
Ministan tsaro Badaru Abubakar ne fadi haka a hirarsa da RFI a ranar Talata, ya kuma bayana cewa tuni shirin ya kama aiki.
“Mun kaddamar da bayar da horon ga dakaru 800 kashi na farko da ake kira “Special Elite Force” kuma wasu 800 za su biyo baya. Dakarun za su samu horo yadda ya kamata da kayan aiki domin yin aiki na kundun bala”. In ji shi
Ministan Tsaro ya kuma ce, za su karbi duk dan ta’addan da ya ajiye makaminsa tare da neman sulhu da gwamnati. Amma gwamnati ba za ta roke su domin yin sulhu ba.
Sannan ya yi kirarin cewa ana samun saukin matsala tsaro, a don haka ya bukaci al’umma da su mara wa sojoji baya a yakin da suke yi da ‘yan ta’adda a duk fadin kasar.