
Daga Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bukaci alhazan jihar nan su kaucewa duk wani abu da zai janyo musu abin kunya yayin gudanar da aikin hajjin bana.
Gwamnan na wannan jawabi ne a Lahadin nan yayin rufe bitar Alhazan Jihar nan.
A ranar Talata 13 ga watan Mayun da muke ciki ne maniyatan jihar nan za su fara tashi zuwa kasa mai tsarki.
Kimanin mutane dubu 3,335 ake sa ran zasu sauke farali daga jihar Kano.
Abba Kabir Yusuf ya ce a bana gwamnati ta ninka malamai masu wa’azi, da likitoci wadanda zasu rinka taimakawa alhazan jihar Kano.
Ya ce a bara alhazan Kano ne suka ciri tuta wajen samun kulawa da tarbiya da kuma tsaftar muhalli.
Ya ce a bana sun samarwa alhazai masauki mai inganci dake kusa da harami ta yadda zasu samu damar yin ibada yadda yakamata.
Ya ce sun gwamnatin Kano ta samar da asibiti na musamman da zasu lura da alhazan jihar nan a kasa mai tsarki.
Ya bukace su da su tattala kudin su har zuwa lokacin da zasu kammala aikin hajji.
Ya ce gwamna ya ware kudaden da za a baiwa mahajattan Kano da zarar sun kammala aikin hajji kafin dawowa Najeriya.
Abba Kabir Yusuf, ya ce zai biya karin kudi da akayiwa maniyata akan abinda suka biya.
A nasa jawabi shugaban hukumar jin dadin alhazai na Kano, Laminu Rabi’u Dan Bappa, ya ce sun biya hukumar alhazai ta kasa naira biliyan 24 da miliyan 500 wanda hakan yasa bata bin su ko sisi.
Ya ce sun baiwa maniyatan dukkan kayayyakin da suke bukata sai dai ya ce suna bin hukumar alhazai ta kasa bashin biza ta maniyata 347.
Ya ce zasu fara jigila da maniyatan da suka fito daga Tudun Wada da Duguwa da Bebeji da Garin Malam da kuma Rimin Gado.