Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bukaci ya yi tattaunawa ta neman sulhu da shi da Ukraine, bayan cikar wa’adin tsagaita wuta na kwanaki uku da ya ayyana.
Rundunar tsaron sama ta Ukraine ta yi kokarin dakile sabon hari ta sama da Rasha ta kai kan birnin Kyiv, kamar yadda magajin garin birnin, Vitali Klitschko, ya bayyana, bayan da rundunar sojin sama ta Ukraine ta yi gargadi kan yiwuwar harin jiragen sama marasa matuka a babban birnin kasar.
A bangare guda kuma, shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ba da shawarar ci gaba da tattaunawa kai tsaye da Ukraine.
A wata hira da manema labarai da aka yi da shi a safiyar wannan Lahadi, Putin ya bayyana cewa tattaunawar ya kamata ta kasance domin samun zaman lafiya mai dorewa da kuma magance tushen rikicin.
Putin ya ce, suna ba da shawarar cewa hukumomin Kyiv su dawo kan teburin tattaunawa a ranar Alhamis 15 ga Mayu a Istanbul na Turkiyya, yana mai cewa wadanda suke son zaman lafiya na gaskiya ba za su ki amincewa da wannan tayin ba.
Sai dai bai ce komai kan bukatar shugabannin Jamus, Faransa, da Poland ta tsagaita wuta ta kwanaki 30 ba.
Ba wannan ne karon farko da Putin ya danganta tsagaita wuta da bukatar magance tushen yakin da ya tayar ba.
Sau da yawa yana gindaya sharudda da suka hada da dakatar da fadada kungiyar tsaro ta NATO, haramta wa Ukraine zama mamba na wannan kungiyar hadaka ta tsaro, cire shugaba Volodymyr Zelenskyy daga kan mulki da kuma mayar da Ukraine karkashin tasirin Rasha.
