Babbar Kotun Kano ta umarci gwamnatin jiha ta biya kamfanin ‘Lamash Properties’, Naira milyan dubu takwas da dari biyar da goma sha daya, a matsayin diyyar gine-ginen da ta rushe a filin Daula Otal.
Kotun karkashin Mai Shari’a Sunusi Ma’aji, ta kuma umarci gwamnatin Kano da gwamnan Abba Kabir da kuma Babban Lauyan Gwamnati, su biya karin Naira miliyan 10 a matsayin kudin shigar da kara.
Kamfanin Lamash ya shigar da kara kotun ne dangane da gine-ginen da aka rushe ba tare da wani dalilin doka ba a watan Yunin 2023, bisa umarnin gwamna Abba Kabir Yusuf.
Masu karar sun bayyana wa mai shari’a Ma’aji cewa, sun mallaki wannan fili ne ta hanyar yarjejeniya da gwamnatin Kano karkashin mulkin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje.
Lauyan kamfanin Nureini Jimoh, ya nemi kotu ta tabbatar da yarjejeniyar da aka kulla tsakaninsu da gwamnatin Kano domin ayyukan kasuwanci a filin na nan daram
Ibrahim Wangida da Bashir Muhammad, Lauyoyi masu kare gwamnati sun bayar da shaida, kamar yadda takardun kotu suka nuna.
Maishari’a Ma’aji ya amince da bukatun masu kara, ya tabbatar da cewa yarjejeniyar da aka kulla na kan doka.
A watan Satumbar 2023, Babbar Kotun Tarayya da ke nan Kano ta umarci gwamnatin jihar ta biya milyan 30,000 saboda rushe gine-ginen da ke filin idi na Kofar Mata.