
Makarantar Prime College a Kano ta yi watsi da umarnin hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu na dakatar da ayyukanta saboda karin kuɗin makaranta.
A watan Yulin da ya gabata ne makarantar ta sanar da karin kuɗin makaranta na zangon karatun 2025/2026, tare da hujjar cewa hauhawar farashin kayayyaki, da kula da ingancin koyarwa da kuma gyare-gyaren kayayyakin makaranta ne suka tilasta hakan.
A wata sanarwar da shugaban hukumar makarantar ta Prime, Aliant Qais Conrad Laureate ya fitar ya ce kafin daukar matakin fiye da kaso 94 cikin 100 na iyaye sun amince da karin, inda mutane kalilan ne ba su amince da karin ba.
Makarantar ta kira matakin rufe ta a matsayin cin zarafi.
A cewar sanarwar kafin rufe makarantar shugaban hukumar kula da makarantu masu zaman kansu ta Jihar Kano Baba Abubakar Umar, ya ziyarci makarantar tare da wasu daga cikin iyaye, inda aka kafa kwamiti na rikon kwarya na PTA mai wakilan iyaye da malamai.
Kwamitin ya kada kuri’a ya kuma amince da karin kuɗin makarantar.
Duk da haka, hukumar ta sake bayyana cewa tattaunawar ba ta kammalu ba, tare da bayar da umarni a soke karin kuɗin.
A cewar Prime College, kotun majistare ta Kano ta bayar da hukunci na dakatar da aiwatar da sabon karin kuɗin makaranta, amma ba ta bayar da umarni na rufe makarantar baki ɗaya ba, kamar yadda aka wallafa a jaridun kafafen sadarwa.
Makarantar ta ce ta garzaya kotu domin kare kanta, tana mai cewa hukuncin zai sanya ɗalibai su rasa karatu
Sanarwar ta roki gwamna Abba Kabir Yusuf ya shiga tsakani.
Idan za a iya tunawa shugaban hukumar kula da makarantu masu zaman kansu ta Jihar Kano Baba Abubakar Umar ya bada umarni a kai karar duk wata makaranta da ta kara kuɗi domin daukar mataki.