
Lamarin ya faru ne a yankin arewacin Ruweng a farkon mako a lokacin da matasan suka sace raguna kafin jami’an tsaro su kai dauki, a cewar Simon Chol Mialith Ministan Yada Labaran yankin.
“Matasa dauke da makamai ne suka kai farmaki, jami’an tsaro sun yi kokarin kare birnin, amma sai matasan dauke da makamai suka mamaye su.” in ji wani jami’in yankin.
Dakarun tsaron Sudan ta Kudu sun fatattaki maharan a ranar Laraba, wanda hakan ya samar da kwanciyar hankali a yankin, a cewar Mialith.
Duk da cewa kafofin yada labaran cikin gida sun ruwaito cewa wasu daga cikin wadanda aka kashe ‘yan kungiyar ne, kamfanin dillancin labaran AFP bai tabbatar da sahihancin wannan rahoto ba.
Hare-haren da ake dangantawa da satar shanu da rikice-rikicen kabilanci na ci gaba da zama barazana ga zaman lafiya a wasu yankunan Sudan ta Kudu, duk da kokarin gwamnati na shawo kan matsalar.
Hukumar tsaro da shugabannin yankin na ci gaba d nazari kan yadda za a dakile irin wadannan hare-hare da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.