Babbar jam’iyar adawa ta PDP ta ƙaddamar da kwamitin gudanar da taronta na ƙasa mai mambobi 119, inda shugabannin jam’iyyar suka yi gargaɗin cewa ba za su sake lamintar wani yunƙuri ya ruguza taron ba.
Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum da shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, Bala Mohammed sun tabbatar da cewa jam’iyyar ta shirya tunkarar gudanar da taronta na ƙasa ba gudu ba ja dawa.
Sai dai kuma ɓangaren ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya fitar da sabbin sharuɗɗa kafin gudanar da babban taron jam’iyyar da zai gudana a ranar 15 da 16 ga Nuwamba, 2025, wanda aka tsara za a yi a garin Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo.
PDP ta tsinci kanta cikin rikici tun bayan gudanar da zaɓen fid da gwani na shugaban ƙasa a 2023, wanda ya fitar da tsohon mataimakin shugaba ƙasa, Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.
Bayan fitowar Atiku, wanda ya zo na biyu ya kasance gwamnan Jihar Ribas a lokacin, Nyesom Wike, ya samu goyon bayan wasu daga cikin gwamnonin abokansa, Wanda suka kafa ƙungiyar G-5 don yin aiki tare wajen yaƙar Atiku.
Wike ya goyi bayan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a wani mataki da ya samu matsayin ministan Babban Birnin Tarayya Abuja. Duk da yake har yanzu shi mamba ne na PDP, Wike ya kasance yana bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar yayin da yake kuma yin aiki don sake zaɓen Tinubu, wani matsayin da yawancin mambobin PDP ba sa jin daɗinsa.
