Daga Fatima Hassan Gagara
Fitacciyar jarumar Kannywood, Zahra’u Saleh Pantami, wacce aka fi sani da Adama a shirin wasan Dadinkowa, ta bayyana babban abin da take tuna Malam Nata’ala da shi.
Jarumar ta bayyan hakan ne a hirarsu ga wakiliyar Premier Radio kan yadda da ji rasuwar marigayin dake fitowa a mijinta a shirin mai farin jini na tashar Arewa24.
Adama ta ce, fim din barkwanci Nata’ala ke yi, amma a zahiri mutum ne mai son barkwanci kuma yana da kyakkyawar mu’amala, ta kuma bayyana yadda hankalinta ya tashi da jin labarin rauwarsa.
Babban abin da ba za ta manta da Malam Nata’ala ba, shi ne kyautar bazatar da ya yi mata a lokacin da shugaban Nijar ya aiko masa da kudi yana tsaka da rashin lafiya a asibiti a Maiduguri.
“Ina zaune ya ce in turo da akawun, sai nace malam wane irin akawun, mai a za a, yi? Sai ya ce, ke dai ki aiko mana. Da na aika, sai na ga ya aiko da min da Naira 200,000. Da na ga kudin sai na ce mai za a siyo maka?
“Sai ya ce, na baki ne kya yiwa yara cefane. Wannan abu ba zan manta da shi ba”.
Duk da cewa Adama ta alakanta wannan kyauta da kasancewar tana daga cikin wadanda ke kan gaba wajen yin bidiyo da kiraye-kiraye musamman ga gwamnan Yobe na ya kawo masa dauki a lokacin da kudin da ake yi masa maganiya kare.
Amma kyakkyawar mu’amalarsa ce da kuma irin zuciyar da yake da ita na alheri ne ya kawo hakan. ta kuma ta yi mamaki kwarai ta kuma yi masa godiya.
Yakubu Mato wanda aka di sani da Nakunduba ko kuma Malam Malama Nata’ala ya rasu ne a asibitin koyarwa na Maiduguri bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Ya rasu ya bar mata ‘ya ‘ya da kuma dinbin masoya a ciki da kuma wajen Najeriya.
