
Kwastam a jihar Kebbi tace ta samu nasarar kama wasu kayan da aka shigo da su ta barauniyar hanya na darajar kudin su yah aura sama da Naira miliyan dari a watan Satumba.
Shugaban hukumar a shiyyar Kebbi, Mahmoud Matawalle-Ibrahim ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya gudanar a Birnin Kebbi ranar Larabar.
“Kayan da aka kama sun haɗa da lita 35,725 na man fetur da buhunhuna 100 na shinkafar waje da katan 140 na taliya da jarkoki 20 na man gyada da buhunhuna 100 na kayan sawa, da kuma buhuna 444 na tabar wiwi.” In ji shi.
Shugaban ya kuma ce, hukumar ta nasarar hakan ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin jami’anta da kuma Sashen Yaki Da Fasa Kwabri na Zone B, wanda ke yaki da fasa kwaurin da fitar da man fetur ta barauniyar hanya.
Bayan haka hukumar ta kuma tara kudaden shiga na sama da Naira miliyan 25.6 a watan Satumbar.