Lauyan gwamnatin Kano ya bayyana hukuncin da Babbar Kotun jihar ta yanke na biyan Naira Biliyan 80 ga kamfanin Lamash kuskure ne.
Barista Wangira ya bayyana hakan ne a hirarsa da wakilin Premier Radio ta wayar tarho ranar Laraba.
Lauyan ya lissafo kurakurai a hukuncin da Mai Shari’a Sunusi Ma’aji ya yanke wanda a cewarsa, ba sa kan tsari na shari’a da za su kai ga yanke wannan hukunci.
“Hukunci ne wanda aka yanke shi ba bisa ka’idar cancantar mai kara da wanda ake kara ba, hukunci ne da aka yi shi saboda wandanda ake kara ba sa kotu a lokacin da ta zauna don ta saurari karar”. Inji shi
Lauyan ya ce, sun shigar da korafi kan hurumin kotun na sauraron karar kasancewar ana sauraronta a wata kotun tun shekara ta 2018.
Amma da aka aiko mi shi da takardar sammacin zaman kotun sai aka kai takardar wani adireshi na daban.
“Ni ofishina ya na kan titin Zariya a Kano amma an dauki takardar sammaci na sauraron karar an kai shi Lamido, wanda Lamindo ba nan ofishina yake ba, don haka ban san lokacin da Kotu za ta zauna ba”. inji shi.
Lauyan ya kuma ce, da kotu ta zauna ta kori karar sukar da suka yi na rashin hurumi, ba tare da kariya ba daga gare su, domin ba sa nan.
“Da muka samu labari sai muka rubuta ‘motion’ na ta soke wannan zaman domin sammacin da aka kai ba ni aka kai wa ba, wani wurin aka kai.
“Kotu ba ta surari wannan ‘motion’ din nawa ba, sai ta ce ta riga ta rubuta hukuncinta.” Inji shi
Barista Wangira ya ce, tuni suka bukaci kotun da ta soke hukuncin da ta yi, ta kuma dakatar da aiki da hukuncin domin an yi shi ne kan lauyoyin mai kara ba su zo ba, duk da cewa karar na gaban wata kotu.
Gwamnatin Kano ba ta ce komai ba dangane da wannnan hukunci na kotu