Zaɓen sabon Fafaroma ya ci tura a zaman farko, bayan fitowar baƙin hayaki daga Sistine Chapel, alamar babu wanda ya samu rinjaye.
Dubban mabiya addinin Katolika daga sassa daban-daban na duniya sun taru a harabar Fadar Vatican domin kallon wannan al’amari na tarihi.
Tunanin da yawa ke yi shine za a iya samun sabon jagora a zaman farko, amma fitowar baƙin hayaki da misalin ƙarfe 9 na dare agogon birnin Rome ya karya wannan fata.
Zaɓen, wanda aka fi sani da conclave, yana gudana ne cikin tsauraran matakan tsaro da tsare sirri.
Limaman darikar Katolika 133 da ake kira Cardinals, wadanda suka fito daga ƙasashe 70, sun kulle kansu a cikin Sistine Chapel domin wannan muhimmin aiki na zaɓen shugaban cocinsu na 267 a jerin shugabannin cocin Roman Katolika.
Wannan sabon zaɓe na zuwa ne bayan rasuwar Fafaroma Francis a watan jiya yana da shekaru 88 a duniya, wanda ya jagoranci mabiya sama da biliyan 1.4 a duniya tun daga shekarar 2013.
Kafin fara zaɓen, kowanne daga cikin limaman ya rantse da littafin Baibul cewa zai kare sirrin duk abin da ya gani da ya faru a yayin zaɓen har karshen rayuwarsa.
Haka kuma, an kwace duk wata na’ura mai tafiyar da sadarwa daga hannunsu, ciki har da wayoyin hannu, domin kare tsare-tsare daga shiga hannu ko tasiri daga waje.
Zaɓen sabon Fafaroma na buƙatar kuri’u 89, wanda ke nufin rinjaye na kashi biyu bisa uku daga cikin dukkanin masu kada kuri’a.
Tunda hakan bai samu ba a zaman farko, za a ci gaba da kada kuri’u a ranar Alhamis, har sai an fitar da sabon jagoran ruhaniya na darikar.
Wannan na nuna cewa mabiya darikar Katolika za su ci gaba da jiran kyandir mai hayaki fari, alamar nasarar zaɓen sabon Fafaroma.
