Shirin haɗakar siyasa tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP zaɓen 2023, Peter Obi, da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, domin tsayawa takara tare a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, na dab da kammala.
Binciken da jaridar PUNCH ta gudanar ya nuna cewa Obi da Kwankwaso sun kafa kwamitin da zai tabbatar da gadewarsu domin samun tikitin shugaban ƙasa da mataimakinsa a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Wani babban jami’i a ADC ya bayyana cewa tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ne ya fara gabatar da shawarar haɗakar Obi da Kwankwaso. A cewarsa, Obasanjo ba wai kawai ya amince da sauya shekar Obi zuwa ADC ba ne, har ma ya shawarci tsohon gwamnan Anambra da ya haɗa kai da Kwankwaso domin samun tikitin shugaban ƙasa da mataimaki a jam’iyyar.
Rahotanni sun nuna cewa Obasanjo bai ɓoye rashin amincewarsa da burin tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar, na sake tsayawa takarar shugaban ƙasa ba.
A halin yanzu, Atiku Abubakar, Peter Obi da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, su ne ‘yan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, yayin da ake cigaba da ƙoƙarin shawo kan Kwankwaso ya shigo jam’iyyar.
Ko da yake Kwankwaso bai shiga ADC a hukumance ba, amma wasu rahotanni na cewa Kwankwason Ka iya tsallakawa zuwa ADC mako mai zuwa
