Gidan Radion Premier na gudanar taron Arewa Ina Mafita don tattauna matsalolin tsaro da sauran al’amuran dake damun yankin.
Taron na gudana ne a dandalin gabatar da wasanni na harabar gidan radiyon da ke unguwar Nassarawa a babban birnin jihar Kano.
Manyan masana ne a fannoni daban-daban ke halartar taron
Za kuma ku iya saurara kai-tsaye daga wannan shafi da kuma shafin dandalin sada zumunta na Facebook.
