Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa an sake baiwa kamfanin Infoquest Nigeria Limited bangaren da aka soke na babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.
Idan dai ba a manta ba gwamnati ta soke sashe na 2 na hanyar da ta hada Abuja zuwa Kaduna daga kamfanin Julius Berger saboda takaddamar farashin.
Da yake jawabi a lokacin da ya duba hanyar, Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya ce an ba kamfanin kwangilar ne don ganin an kammala aikin cikin sauri.
Da yake bayyana dalilin da ya sa aka soke kwangilar wannan sashe daga hannun Julius Berger, Ministan ya ce kamfanin Julius Berger ya rage saurin aikin, sannan ya rubuta wasika ga ma’aikatar ayyuka ta tarayya inda ta bukaci a sake kara masa kudi naira biliyan 797 zuwa naira tiriliyan 1.5, hakan ya sanya gwamnatin tarayya ta kwace aikin.