
Shugaban mulkin soja dan asalin jihar Kano da ya assasa Abuja da wasu manyan ayyuka na ci gaban kasa
A irin wannan rana ce 13 ga watan Fabarairun 1976 a ka kashe Janar Murtala Muhammad shugaban Najeriya na mulkin soja.

An kashe shugaban ne a jihar Legas fadar gwamnatin tarayya a waccan lokaci a wani yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.
Dan asalin jihar Kano, Janar Murtala Ramat Muhammad ya zama gwarzon shugaba wanda tarihi ba zai taba manta wa da shi ba, sakamakon irin ayyukan alheri da yayi a cikin kwanaki 200 yana mulki.

Wasu muhimman abubuwan da ya assasa:
- Kirkiro jihar Kano: Shi ya kirkiro jihohi 12 daga jihohi uku na kasar da kuma tsarin lardi-lardi.
- Kafa Abuja: shi ya fara tunanin dauke fadar gwamnatin tarayya daga Lagas, a inda ya kafa kwamitin gano inda za kai fadar gwamnatin Najeriya daga Legas
- Yaki da cin hanci da rashawa: Ya fito da tsare-tsare a aikace na yin hakan.


Wasu wuraren da aka sa sunan Murtala Mohammed don tunawa da shi.