
Sakataren gwamnatin jihar Kano, Umar Farouk da kwamishinan matasa da wasanni Mustpha Rabiu Musa Kwankwaso da sauran tawaga daga gwamnatin Kano ne suka jagoranci bikin kaddamar da shirin fara tunkarar gasar wasanni ta kasa da za ta gudana a jihar Ogun.
Aza harsashin kunna wutar dai al’ada ce da kowacce jiha da za ta fafata a gasar sai ta yi, domin tunkarar gasar wasanni ta kasa da ake gudanarwa a kowacce shekara.
A kwanakin da suka gabata ma, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kansa, ya jagoranci kaddamar da tambarin shirin fara gasar wasanni ta kasa da za a yi.
Ana saran jihar Ogun ce za ta karbi bakuncin gasar wasanni ta wannan shekarar da za a yi daga 16 zuwa 30 ga Mayun 2025.
Kuma tawagar jihar Kano na daga cikin tawagar da ta yi shirin halartar gasar a yunkurin lashe lambobin yabo na zinare, tagulla da kuma a zurfa.