Sama da mutane dubu 250 ne ƙungiyar agaji ta Red Cross ta tabbatar sun ɓata a fadin duniya, lamarin da suka ceya ƙaru da kashi 70 a cikin shekaru biyar da suka wuce.
A wata sanarwa, kungiyar Red Cross ta ce ƙaruwar wannan adadi na mutanen da ke ɓacewa baya rasa nasaba da ta’azzarar rikice-rikice, yawan ƙaurar jama’a da kuma rashin mutunta dokokin yaƙi.
Ƙungiyar ta ce ƙaruwar masu ɓacewa bat na nuni da yadda hukumomin da aka ɗora wa alhakin kariya, da ɓangarorin da ke yaki da juna su na gaza kare waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.
Sanarwar ICRC ta ƙara da cewa yarjeniyoyin Geneva, wanda ke cikin jerin yarjeniyoyin da aka cimma a sshekarar 1949 bayan yaƙin duniya na biyu ya tanadi cewa a taimaka wajen kauce wa rabuwar iyalai, amma sannu a hankali an fara daina mutunta hakan.
Mutane dubu 284,400 ne aka sanar sun ɓata a ƙarshen sshekarar 2024,wato adadin ya tashi daga dubu 169,500 a shekarar 2019, kuma an ɗora alhakin hakan ne akan rikicin Sudan, Gaza da Ukraine da sauran dalilai.
Ƙungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent su na aiki sau da ƙafa domin nemo mutanen da suka ɓata a fadin duniya, inda suke sada su da iyalansu idan suka same su.
Wani lokaci ana yin dace, saboda a shekarar da ta gabata, mutane dubu 16 ne aka gano.
