
Ahmad Hamisu Gwale
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta fara aikin gyara layin dogon Abuja zuwa Kaduna wanda ya lalace sakamakon hatsarin jirgin kasa.
A ranar Talata da ta gabata ce jirgin mai tarago 10 da ya tashi da misalin karfe 11:00 na safe daga tasharsu da ke Kubwa a Abuja da nufin zuwa Kaduna, ya rikito daga kan hanyarsa a wata ƙaramar tasha da ke kauyen Asham.
NRC tace ta bayar da aikin gyaran ne ga wani kamfanin ƙasar Sin wanda kuma ya fara aikin gyaran a ranar Laraba da ta gabata.
An dai kai taragu ukun ne zuwa babban tashar hukumar da ke yankin Idu a Abuja, a yayin da a ke saran ɗauko ragowar shidan da kuma injin jirgin a ranar ta Alhamis, kamar yadda majiyoyi suka bayyana.