
Hukumar Wayar da Kan Al’umma ta Najeriya NOA ta sanar da sabbin ka’idoji game da yadda za’a rera taken ƙasa a taruka da shagulgulan gwamnati a faɗin ƙasar.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar, NOA ta bayyana cewa daga yanzu ana buƙatar a rera baitin farko ne kawai na taken ƙasa a dukkan tarukan gwamnati, maimakon baitoci uku gaba ɗaya da aka saba yi.
Sanarwar ta ƙara da cewa baitoci uku na cikakken taken ƙasa za’a dinga rera su ne kawai a lokuta na musamman.
Ga dai karin bayanin da Darakta Janar na Hukumar NOA reshen jihar Kano Alhaji Rabi’u Ado ya yi.
Hukumar ta ce matakin ya biyo bayan buƙatar daidaita yadda ake gudanar da taken ƙasa da kuma farfaɗo da al’adun kishin ƙasa a tsakanin ‘yan Najeriya, musamman matasa.
NOA ta jaddada cewa sabon tsarin zai taimaka wajen tabbatar da nutsuwa, ladabi da girmamawa a yayin rera taken ƙasa a dukkan wuraren taro na gwamnati da na jami’ai