
Ma’aikatar Ilimi ta Kasa ta dakatar da shugabannin manyan makarantun sakandire na gwamnatin tarayyya Unity Schools biyu saboda rashin bin ka’idojin ciyar da dalibai.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktar Yada Labarai na ma’aikatar, Boriowo Folasade ta fitar. ta kuma ce gwamnati ta yi hakan ne a kokarinta na tabbatar da jin dadin dalibai a makarantun.
Sanarwar ta ce, matakin ya biyo bayan wani bincike ne da ya gano makarantun ba sa ba da abinci mai inganci ga dalibai.

Foloshade ta ce, an tura manyan jami’ai domin bibiyar yadda ake gudanar da ciyarwa a makarantun dake karkashin gwamnati.
Sanarwar ba ta bayyana sunayen makarantun da abin ya shafa ba da kuma shugabannin ta kuma ce, gwamnati ta ce za a gudanar da bincike mai zurfi tare da daukar matakan da suka dace.