Ƙungiyar Ƙwadago ta Kasa (NLC) ta bukaci ’yan Najeriya da su ƙi amincewa da dokokin haraji da ta ce an yi musu “cushe” ko sauye-sauye ba tare da tsari ba.
Shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero, ne ya bayyana haka a cikin saƙon Kirsimeti na shekarar 2025.
Ajaero ya ce dokokin da aka gaggauta yi suna ɗauke da kura-kurai, don haka ya zama wajibi a sake tsara su cikin tsari da adalci.
Ajaero ya jaddada cewa ya kamata ’yan ƙasa su kasance masu haɗin kai domin tabbatar da cikakken adalci a dukkan al’amuran da suka shafi mulki da gudanarwar ƙasa.
“Doka mai kyau ita ce wadda aka tsara cikin tsari, ba wadda aka yi da gaggawa ta ɗauke da kura-kurai,” in ji Ajaero.
A halin yanzu, Majalisar Wakilai ta kafa wani kwamiti na musamman domin bincikar batun harajin.
Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Honourable Mukhtar Aliyu Betara, ya fara bincike tun ranar 23 ga watan Disamba, tare da alƙawarin kammala aikin cikin lokaci.
