Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NIMET) ta yi hasashen cewa Najeriya za ta fuskanci matsanancin zafi sakamakon dumamar yanayi, lamarin da ke shafar jihohi da dama a faɗin ƙasar.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a ranar Alhamis.
Ta kuma ce, daga ranar Laraba 19 ga Fabrairu, an samu matsakaicin zafin da ya kai tsakanin digiri Celsius 38 zuwa 40 a wasu sassan ƙasar.
Bisa ga rahoton NIMET, garuruwa irin su Fatakwal, Owerri, Enugu, Awka, Bidda, Minna, Gusau, Iseyin, da babban birnin tarayya Abuja sun fuskanci yanayin zafi mai tsanani da ya kai digiri Celsius 38.
Haka nan, Sokoto, Kebbi, Lokoja, Makurdi, Abakaliki, Ikom, Jalingo, da Yola sun sami ƙarin zafi mai tsanani, wanda ya haura digiri Celsius 39.
A wata tattaunawa da wakiliyarmu, Safina Abdullahi Hassan, wani mai rajin kare muhalli, Umar Sale Anka, ya bayyana wasu daga cikin manyan dalilan da ke haddasa sauye-sauyen yanayin da ake fuskanta.
Hukumar ta NIMET ta shawarci ‘yan ƙasa da su kare kansu daga illolin zafi mai tsanani ta hanyar shan ruwa da yawa, gujewa yawan fita rana, da kuma amfani da kayan sanyi don rage haɗarin rashin lafiya da ka iya tasowa.
