Shugaban gwamnatin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani, ya zargi ƙasashen ƙetare da haifar da tsaiko wajen ci gaban ƙasar, don haka ya buƙaci al’ummar ƙasar su ci gaba da addu’a.
A lokacin da ya ke yiwa al’ummar Nijar jawabi a kafafen radio da talabijin game da cika shekaru 2 da hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum, ya ce katsalandar ɗin da ake yiwa ƙasar daga waje ne ke maida hannun agogo baya, game da tsare-tsaren ci gaban da gwamnatinsa ke da shi.
Duk da cewa Tiani ya nuna rashin jin daɗinsa kan halin matsin da ƴan ƙasar ke ciki, sai dai bai ce komai game da sojoji da fararen hular da suka rasa rayukansu a baya-bayan nan sanadiyar hare-haren ƴan ta’adda.
Shekaru biyu ke nan bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar, amma har yanzu hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum da mai ɗakinsa na ci gaba da tsare a fadar shugaban ƙasar, duk kuwa da ƙoƙarin shiga tsakani da aka yi don sakisu.
Sai dai tun bayan juyin mulkin da sojojin suka yi a ƙasar, tattalin arzikinta na kwan gaba kwan baya, musamman a ɓangaren hada-hadar banki da hauhawan farashin kayayyaki, duk da cewa masa na ganin an samu ci gaba ɓangaren hako mai da kuma aikin noma, wanda yasa a shekarar da ta gabata tattalin arzikin ƙasar ya ƙaru da kashi 8.4
