Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar kano, ta bayyana damuwar ta kan karancin jami’ai mata a hukumar, inda tace hakan na kawo cikas ga gudanar da ayyuka musamman waɗanda suka shafi harkokin mata.
Kwamandan hukumar, Dahiru Yahaya Lawal, ne ya bayyana hakan, a yayin wani taro da cibiyar Isa Wali Empowerment Initiative, ta shirya a hukumar jiya talata, domin inganta rayuwar mata.
Dahiru Yahaya, yawaitar shigar mata harkar ta’ammali da miyagun kwayoyi, ne yasa hukumar yunkurin kiran mata shiga ayyukan hukumar, domin samun sauki yaki da harkar.
Taron ya samu halartar, mata da matasa daga kungiyoyi daba-daban, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi hakkokin mata, adalci da kuma daidaito.
