
Hukumar hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama wani ɗan kasuwa da kwayoyi 127 da ya hadiye ya kuma cusa wasu a duburarsa.
Dan kasuwan mai suna Ejiofor Godwin Emeka mai shekaru 52, an kama shi ne a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano a karshen mako.
Ejiofor dan kabilar Igbo, yana da shagunan sayar da kaya a biranen Lagos da Onitsha a jihar Anambra, ya iso Najeriya ne daga birnin Bangkok ta kasar Thailand a jirgin Ethiopia ranar Laraba, 8 ga Oktoba, 2025.
Hukumar NDLEA ta kama shi ne bayan samun sahihan bayanan leƙen asiri game da aikata laifin safarar miyagun kwayoyi.
Bayan isowarsa, an kai shi dakin bincike inda na’urar duba jiki (body scan) ta tabbatar da cewa ya hadiye wasu kwayoyi kuma ya boye wasu a cikin al’aurarsa.
An gano fakiti 58 na kwayoyin cikin wandonsa, sannan aka shiga bin diddigin abin da ke cikin cikinsa ta hanyar sa masa ido har ya fara fitar da sauran kwayoyin.
A cikin ‘yan kwanaki wanda ake zargin ya fitar da fakiti 69 ta hanyar bayan gida, wanda ya kai jimillar fakitin da samu a wurinsa zuwa 127.