
Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ta doke ta kasar Rwanda da ci 2 mai ban haushi ya faranta wa kowa a kasar shin ko hakan zai dore?
A ranar Juma’a ne kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta doke ta Rwanda da ci 2-0 a birnin Kigali a wasannin neman gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya.
Ɗan wasan Najeriya Victor Osimhen ne ya zura duka kwallayen biyu gabanin hutun rabin lokaci, wanda har aka tashe Rwanda ba ta farke ba.
Nasarar da ta kai Najeriya matsayi na huɗu a cikin ƙasashe shida da ke Rukunin C bayan wasanni biyar-biyar.
A wasan Najeriya na gaba, za ta fafata ne da ƙasar Zimbabwe a fiin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo a jihar Akwa Ibom a ranar Talata mai zuwa.
Bayan doke tawagar ƙasar Lesotho da Afirka ta Kudu ta yi ranar Juma’ar, yanzu ta ƙara tsawaita jagorancin rukunin da ta ke yi zuwa maki 10.
Sai Benin da ke ta biyu da maki takwas, Rwanda ta uku da maki bakwai, sai kuma Najeriya mai maki shida.
Wasanni huɗu suka rage wa Najeriya yanzu, waɗanda a cikinsu ne za ta nemi ɗarewa saman teburin. Amma za ta buƙaci doke Afirka ta Kudu da Benin kafin ta yi hakan.
- 1 ga Satumba: Nigeria da Rwanda
- 8 ga Satumba: Afirka ta Kudu da Najeriya
- 6 ga Oktoba: Lesotho da Najeriya
- 13 ga Oktoba: Najeriya da Benin
Yanzu Najeriya na da sauran wasa biyar, duk da wanda za ta fafata da Zimbabwe a mako mai zuwa.
Ko wannne fata za ku yi mata?